Hoto da zane
Tambaya
Mene ne hukuncin yin hoto da zane?
Amsa
Hoto da zane suna cikin fannoni masu kyai da suke nuna kwarewar dan Adam, su din hanyoyi ne guda biyu masu mahimmanci wajen karantarwa da kiyaye da kuma tabbatar da abubuwa, saboda haka dukansu sun halatta a shari’ance, da sharadin kiyaye ka’idojin dabi’a da na sana’a da ladubbansu wadanda su ne suke iyakance manufar zane da hoto.