Fannin zane

Egypt's Dar Al-Ifta

Fannin zane

Tambaya

Mene ne hukuncin wasu zanunnuka da ake yi a riguna ko bango?

Amsa

Babu laifi ayi hoto da zane ko rubutun barkwanci matukar dai hotunan zanen ba su kunshi abin da bayyana shi ko zana shi haramun bane, kamar dai tsaraici, ko wani abu wanda bai dace ba, ko ingiza mai kantu ruwa kan sabawa umurni na shari’a, ko kuma zuga mutane yiwa shugaba bore, (kamar doka ko shugaba ko daula), idan hutunan ko zanen sun kunshi abubuwan da suka gabata to sun haramta, ba wai don kasancewar su hotuna ba, aa sai don abubuwan da suka kunsa na laifi,  yana daga cikin abin da ya halasta hutunan da aka zana a wurare masu santsi ko abin da ya yi kama da haka, domin abin da yazo daga Abu Dalhat Allah ya kara masa yarda wanda Annabi S.A.W. ya ce: (Mala’iku ba sa shiga gidan da akwai hoto ciki) Busru ya ce: Zaidu bin Khalid ya yi rashin lafiya, sai muka je gaishe shi, sai muka ga wani labure a gidansa na dauke da hutuna, sai na cewa Ubaidullah Al’khaulani , shi bai taba bamu labari akan hotuna ba? Sai ya ce: Eh lallai  ya bamu, sai dai fa banda zanen dake jikin kyalle, shin baka saurare shi bane? Sai na ce : a a, sai ya ce: to bari kaji,  to lallai ya ambata. Anyi ittifaki akansa.

Share this:

Related Fatwas