Mummunan zato

Egypt's Dar Al-Ifta

Mummunan zato

Tambaya

Saurayin da aka yi mana baiko tare yana yawan munana zato kan lamarina, ta ya ya zan iya magance hakan?

Amsa

Lalacewar alaka a tsakanin wadanda aka yi wa baiko sakamakon mummunan zato, da kuma bibiyan sirrikan juna da kuma kokarin gurgunta amincin dake tsakaninsu, to wannan ya saba da hikima da tsari na dabi’un zamantakewa bisa abin da shari’a mai daraja ta sanya wurin shar’anta baikon aure.

Allah Madaukakin Sarki ya yi hani ga bayinsa akan munana zato a wurare da yawan gaske a cikin littafinsa mai girma, daga ciki akwai inda Allah yake cewa: (Ya ku wadanda kuka yi Imani ku nesanci yawan zato saboda wani sashe na zato zunubi ne kuma kada kuyi wa juna bin diddigi) [Al-hujurat:12] Imam ibn Kather ya ce a tafsirinsa, (7/377): Allah Ta’ala ya ce: a cikin wannan ayar, yana hani ne ga bayinsa akan yawaita yin zato, wato shi ne: zargi da ha’inci ga ahali da makusanta da sauran mutane a wurin da ba mahallinsa ba, saboda sashin hakan yana kasancewa zunubi ne, to mutum ya nesanci hakan domin gudun zargi, an samo mana daga Amirul Muminina Umar bin Khaddab – Allah ya kara masa yarda ya ce:– “Lallai kada kuyi zaton wata kalma da za ta fita daga dan’uwanka musulmi face sai alheri domin kaima zaka samawa Kalmar masauki na alheri”

Share this:

Related Fatwas