Mu’amala da banki

Egypt's Dar Al-Ifta

Mu’amala da banki

Tambaya

Mene ne hukuncin bayar da hayar gida ga daya daga cikin bankuna

Amsa

Bayar da hayar gida –da yarjejeniyar haya da aka sani- ga bankuna, akan za a biya kudin haya daidai yake da dukan hayar da ake yi, wannan abu ne da ya halatta, haka ma yin ittifaki akan kudin haya, ko abin da zai kwafe makwafinsa ya halatta ta dukan fuskoki, shari’a ba ta hana haka ba; domin hakan hakkoki ne da suke zuwa sakamakon halattacciyar yarjejeniya. Kuma abu ne da shari’a ta tabbatar cewa asali game da yajejeniyoyin mu’amala shi ne halacci, muddin ba an kawo dalili na shari’a akan haramci ba, ita kuwa haya ta halatta a Alkur’ani da Hadisi da Ijma’i.

Share this:

Related Fatwas