Yanka da inji
Tambaya
Mene ne hukuncin yin yanka da inji?
Amsa
Yin amfani da inji wajen yanka dabbobi abu ne da shari’ar Musulunci ba ta hana ba, idan ya zamana akwai wuka ko abin da ya yi kama da wuka da zai yanke jijiyoyin da wajibi ne a yanke su a lokacin yanka, a kula da yankar ta kasance a kasan wuya, ba ta keya da, sai dai idan mai sauri ne matuka, kaman sara da takobi.