Matakan kafirci

Egypt's Dar Al-Ifta

Matakan kafirci

Tambaya

Shin kafirce mataki- mataki ne, shin ma wai yana da rabe- rabe da akansa ake samun bambance- bambancen hukunce- hukunce?

Amsa

Kaforci shi ne: Inkarin abin da kowa da kowa ya sani cewa yana cikin addinin da shugabanmu Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya zo da shi, Kaman inkarin samuwar mahalicci, da Annabtarsa mai tsira da aminci, da inkarin farillan Musulunci da ya ginu akansu, da halatta abubuwan da aka haramta, wadanda haramcin su ya tabbata da yankakkun dalilai da hujjoji, da makamantan haka, kafirci na zuwa a wasu lokuta da ma’anar butulci.

Kafirci mataki- mataki ne, a cikinsu akwai wanda yake fitar da mutum daga addini, akwai kuma wand aba ya fitarwa daga addini, mutumin da yake aikata sabo za a iya sifanta shi da na biyu, amma ban a farkon ba, kafirci ya kasu gida hudu: kafircin inkari, da na musantawa, da na taurin kai da na munafunci, kaman yanda al- Azhariy ya bayyana, da kafirce wa wanin Allah, wannan kafirci ne da ya saba da kafirci, ma’ana akasin kafirce wa Allah, na farkon yana fitarwa daga addini, da dawwama a cikin wuta, na biyun kuma yana kai wa zuwa ga fasikanci ne kawai, ba ya kai wa zuwa ga dawwama a wuta, misali: mutumin da ya aminci da kadaituwar Allah, da Annabta a harshensa, ya kuma kuduri haka a zuciyarsa, amma yana aikata manyan laifuffuka irinsu kisa, da aikata barna a bayan kasa, da nuna butulci a cikin hakkoki da ni’imomi da makamantan haka, akwai Hadisan da suka ambaci kalmar kafirci akan manyan laifuffuka, irinsu: (Yakarsa kuma kafirci ne) –kaman yanda Imam al- Bukhari da Muslim suka ruwaito-, da Hadisin: (Wanda ya bar sallah da gangan lallai ya kafirta) [al-Dabariy a cikin al- Ausat], da sauransu, duka wadannan Hadisai ana yi masu tawili ne da cewa kafircin da bai kai kafirci ba, hawarijawa ba su da abin doga a cikin wadannan Hadisan akan kafirta wadanda suka aikata manya laifuffuka da suke yi.

Babu wani daga cikin Musulmai a da a yanzu da ya taba cewa aikata manyan laifuffuka suna fitar da mutum daga addini, sabanin hawarijawa da makamantansu da suke kafirta wanda ya aikata manyan laifuffuka, suke fitar da shi daga addini.

Share this:

Related Fatwas