Ma’anar kafirci kafirci

Egypt's Dar Al-Ifta

Ma’anar kafirci kafirci

Tambaya

Mene ne ma’anar kafirta Musulmi? Sannan wane ne aka daura wa alhakin yin hukunci da kafirci ko imani?

Amsa

Addinin Musulunci ya zo ne saboda ya haskaka wa mutane hanya, ya fitar da su daga duhu zuwa ga haske, sai wasu mutane suka yi na’am da shi wasu kuma suka kafirce, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Allah shi ne majibincin al’amurran wadanda suka yi imani, yana fitar da su daga duhu zuwa haske, su kuwa wadanda suka kafirce masu jibintar al’amarinsu su ne dagutai, suna kuma fitar da su daga haske ne zuwa duhu..) [al- Bakra: 257], duk wanda ya amshi Musulunci shi ne mumini, wanda kuma ya ki ya yi girman kai shi ne kafiri, ita Kalmar kafirce a harshen Larabci tana nufin, suturtawa da sakayawa, ana cewa “Kafaran ni’imata”, ya sakaya ni’ima, ma’ana ya yi butulci, shi kafirci kishiya ne na imani, shi kuma kafircin ni’ima kishiya ne na godiya, ana cewa ya kafirce wa kaza, ma’ana ya yi baran- baran da shi, Allah a cikin Alkur’ani yana cewa: (Lallai na yi baran- baran da abubuwan da kuka hada su da ni tun farko) [Ibrahim: 22], idan an ce “kaffarahu” ana nufin ya kafirta shi.

Kafirci a shari’a kuwa yana nufin : inkarin abin da kowa ya san cewa lallai wannan abu yana cikin addinin da sayyiduna Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya zo da shi, alal misali inkarin samuwar mahalicci, da annabatar mai tsira da amini, da inkarin farillan Musulunci da ya ginu akansu, da halatta abubuwan da aka haramta wadanda haramcinsu ya tabbata da yankakkun dalilai, da makamantan haka.

Shi kafirta Musulmi hukunci ne na shari’a da ake sifanta ayyukan wanda yake makalfi ne a wurin shari’a; saboda haka yanke wannan hukunci abu ne da ya takaita da masu bayar da fatawa da alkalai, babu wani da yake da hakki yanke wa mutane wannan hukuncin ba su ba, Imam al- Sibkiy ya ce: shi kafirtawa hukunci ne na shari’a, dalilin da yake sanya a yi shi kuwa shi ne inkarin allantakar Allah, ko kadaituwarsa, ko inkarin sakon Musulunci, ko wata magana ko aiki da shari’a ta hukunta cewa duk wanda ya yi inkarinsu ya kafirta.

Share this:

Related Fatwas