Hatsarin kafirta Musulmi

Egypt's Dar Al-Ifta

Hatsarin kafirta Musulmi

Tambaya

Mene ne hatsarin kafirta Musulmi a cikin al’umma, shin ma wai kafirtawa aikin daidaikun mutane ne?

Amsa

Kafirta Musulmai daya ne daga cikin manyan bala’o’in da suke kacancana tsarin rayuwar al’umma, suka kuma yi aiki wajen dasa rarrabuwar kawuna, da halatta zubar da jini ba tare da hakki ba, lallai shari’ar Musulunci ta bayyana hatsatin kafirta Musulmai, Alkur’ani da Hadisai kuma sun hana aikata haka, Allah mai girma yana cewa: (Kada ku kuskura ku cewa wanda ya yi maku sallama: ‘kai ba Musulmi ba ne’) [al- Nisa’i: 94], a Hadisi kuma Annabi (SallalLhu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Kada wani mutum ya jefi waninsa da fasikanci, kada kuma ya jefe shi da kafirci, in ba haka yake ba, kalmomin za su dawo kansa, idan wanda ya jefa din ba haka yake ba) [al- Bukhari], haka ma (SallalLhu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Abubuwa guda uku suna cikin asali da tushen imani: kamewa ga barin wanda ya furta “La’ilaha illalLahu” kada mu kafirta shi sakamakon aikata zunubi, ba kuma za mu fitar da shi daga Musulunci sakamakon wani aiki da ya aikata ba) [Abu Dawud], lallai malaman Musulunci sun hadu akan cewa ana kafirta mutum ne ta hanyar hukuncin shari’a a kotu, ba aiki ne na daidaikun mutane a cikin al’umma ba, saboda haka, dole ne Musulmi ya kiyaye kansa daga hatsarin kafirta kowa cikin Musulmai, saboda tsananin hatsarin da yake tattare da haka; da abin da yake biyo bayan haka na halatta jini, da lalacewar hakkokin bayin, inda akan fitar da su daga addinin Musulunci.

Share this:

Related Fatwas