Halifan Musulmai
Tambaya
Shin akwai mutumin da zai iya zama halifan Musulmai?
Amsa
Ma’anar halifancin Musulunci –kaman yanda ƙungiyar ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) suke riyawa- kuskure ne da ya saɓa da abubuwan da suke faruwa, ba zai yiwu a aiwatar da shi a wannan zamanin ba, balle kuma a tirsasa wa mutane shi da ƙarfin bindiga, da zubar da jini; wannan ya sanya ƙungiyar ta zama ɓatacciyar ƙungiya da take son ta lanƙwasa ma’anar halifanci wajen biyan buƙatunta, da kuma samar wa munanan ayyukansu da madogara ta shari’a, waɗanda a haƙiƙa ba Musulunci ba ne, hasali ma ba ruwan Musulunci da su.
Lallai tsarin halifanci a Musulunci ya sami cigaba a cikin ƙarnonin da suka shuɗe, bayan faɗaɗar ƙasashen Musulmai, da yaɗuwar Musulunci a cikin mutane, da kuma ƙara yawan ƙasashen da suke rungumi Musulunci a yankunan duniya, tsarin halifanci ma ya sauya akan yanda aka san shi a zamanin hilafa Rashida, wannan abu ne da duk wani mai gani da basira yake iya riska, shi ne yanayin da Musulmai suka rayu a ƙarnoni masu yawa kuma masu tsawo, inda suke cike da shugabanni da sulɗanai, da hakimai da sarakuna.
Lallai a kowane gari, ko wasu adadi na garuruwa akwai shugaba da yake jagorantarsu, haka ma a sauran garuruwan akwai wani shugaba, ko sarki da hukuncinsa ya taƙaita da su, inda ba a la’akari da hukuncinsa a wasu garuruwa, mutanen wannan garin ba su biyayya ga sarki, ko shugaban wancan garin, haka ma na wacan garin ba sa biyayya ga sarkin wannan garin, wannan shi ne yanayin da mutane suka kasance a ciki a tsawon tarihi, kuma hakan ne ya yi daidai da ƙa’idojin Shari’a, ganin irin yanda ƙasashen Musulmai suka ƙara faɗaɗa, suka kuma yi nisa da juna.