Sada zumunci

Egypt's Dar Al-Ifta

Sada zumunci

Tambaya

Ta yaya ake iya sada zumunci?

Amsa

Shi sadar da zumunci yana daga cikin bayyanannun abubuwan da musulunci ya baiwa kulawa wurin karfafa hanyoyin hada kan al’umma, Allah Ta’ala yace: (Kuji tsoron Allah wanda zai tambayeku   akan zumuntarku), ai kar ku yanke zumuntarku.

Sannan Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam ya bayyana  cewa shi sada zumunci da yiwa makusanta biyayya da nuna musu kauna sakamakon haka shine samun albarka a rayuwa da samun karin arziki, sai SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam yace: (Duk wanda ya yake so a yalwata masa arzikinsa ko kuma wanzar masa da gurabunsa to ya sadar da zumuncinsa).

Shari’a tayi hani akan yanke zumunta, inda ta ambaci cewa shi yanke zumunci yana daga cikin siffofin jahiliyya da kuma nesanta daga addinin Allah, domin Allah Ta’ala yace: (shin kuna ganin abune da ya kamata idan kuka juya baya kuma kuna barna a doron kasa kuna yanke zumuntakarku) {Muhammad:22}

Sada zumunci bai takaita akan musanyar ziyarce-ziyarce ba kawai, saidai yana kasancewa ne da wanin hakan cikin hanyoyin sadar da zumuncin, kamar bayar da kyauta da kiran waya, ko yiwa juna wasika ko mika gaisuwa, da wasu hanyoyin na sada zumunta.

Sadar da zumunci ba wai a yake da kawar da kai bane na idan an kyautata maka kaima ka kyautata, ko kuma jiran alheri sannan kaima kayi alherin, abinda akeso shine dawwama wurin sadar da zumuncin ba tare da kana jiran sai anyi maka ba, kamar dai yanda Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam ya bayyana a zancensa: (mai sadar da zumunci bai kasance mai jiran sakamako ba, sai dai shi mai sadar da zumunci shine wanda idan aka yanke masa zumunta yake sadar da ita).

Share this:

Related Fatwas