Hada salloli

Egypt's Dar Al-Ifta

Hada salloli

Tambaya

Mene ne hukuncin hada salloli a lokaci daya sakamakon saukar ruwan sama?

Amsa

Hada salloli kamar azahar tare da la’asar ko magariba da issha’i a lokaci daya na farko sakamakon saukan ruwan sama mai yawa ba tare da kasaru ba ya halasta a shari’ance, hakan na zuwa ne domin saukakawa da cire kunci, saboda a asali dai shi ne wajabta yin sallah a lokacinta ba tare da gaggautawa ko jinkirtawa ba, amma gwama sallah wuri daya a lokaci daya na zuwa ne bisa dalilin togaciya, kuma hakan baya halasta sai da uzuri, saukan ruwan sama mai yawa na daga cikin uzururrukan da ke halasta hada salloli biyu a lokacin farko,tare da lura da sharuddan da malaman fikihu suka bayyana kamar dai samun saukan ruwan sama a farkon lokaci, har zuwa lokacin sallar ta biyu, sannan ruwan ya zama ya yi yawan da zai iya jika riga ga wanda ya fita, abin nufi anan shi ne ya zama za a sha wuya wurin fita zuwa masallacin tare da samuwar hakan, sannan ya zama hada sallolin a lokacin farko ne ba lokacin karshe ba, sannan a kulla niyyar yin sallar a tare a lokacin sallar farko, sannan sallar ta kasance jam’i ne kuma a masallaci, sannan kuma a jere – tsakanin sallar farko da ta biyu – sannan kar a samu tazara mai tsayi tsakanin sallar farko da ta biyu. 

Share this:

Related Fatwas