Hada salloli a lokaci daya

Egypt's Dar Al-Ifta

Hada salloli a lokaci daya

Tambaya

Mene ne hukuncin hada salloli biyu a lokaci daya saboda saukan ruwan sama

Amsa

Hada salloli a lokaci daya kamar azahar tare da la’asar, da kuma magariba tare da issha’i duk a lokacin na farko a tare sakamakon ruwan sama mai tsanani ba tare da tawayesu ba to ya halasta a shari’ance, hakan yana kasancewa ne domin rage tsanani ga masallata, saboda asalin abin da shari’a ta sanya shi ne ayi sallah a lokacinta na asali, don haka hada salloli wuri daya yana kasancewa ne a matsayin togiya, kuma hakan ba ya kasancewa sai da uzuri, saukan ruwan sama mai karfi na daga cikin dalilan da suke sanya yin rangwamen hada salloli biyu a lokaci daya, tare da kiyaye sharudan da malamai suka sanya kafin halascin hakan kamar saukan ruwan sama mai karfi daga lokacin sallar farko tare da tunanin kaiwa zuwa ga lokacin na biyu, karfin saukan ruwan saman ya zama zai iya jika kayan mutum idan ya shiga ciki, wanda hakan ke nuna wuyatan zuwa masallacin saboda samuwar ruwan saman, to daga haka sai a hada sallolin a lokacin na farko ba na karshe ba, tare da kudurta niyyar hada sallolin a lokacin sallatar ta farko, hakanan a lokacin na biyu, kuma ya kasance sallar cikin jam’i ne a cikin masallaci kuma ajere kar ratar da ke tsakaninsu ya yi tsayi.    

Share this:

Related Fatwas