Jariran kwalba
Tambaya
Shin ya halatta a haifi yara ta tsarin jariran kwalba?
Amsa
Haihuwa ta hanyar hada kwayoyin maniyyi na mata da miji a wajen mahaifa, da sake shigar da shi cikin mahaifar matar, abu ne da shari’a ba ta hana ba, muddin dai kwayar halitta an ciro shi ne daga maniyyi matar haka ma maniyyin an ciro shi ne daga mijinta, aka kuma hada sub a a mahaifa ba ta hanyar kwalba, aka kuma sake mayar da shi cikin mahaifar wannan matar, ba tare da an sauya, ko cakuda shi da maniyyin wani mutum na daban, ko kwayoyin halitta daga wata matar ta daban ba, ya kuma zama lallai akwai bukatar a yi haka din a likitance; wajibi ne idan za a yi haka ya zama likita kwararre ne zai gudanar.