Sauraron waka

Egypt's Dar Al-Ifta

Sauraron waka

Tambaya

Mene ne hukuncin sauraron waka, kuma mene ne ka’idan sauraro a shari’a?

Amsa

Lallai ita waka a gaba dayanta ba ta kasancewa abar haramtawa a cikin shari’ar Musulunci, hakika hadisai da yawan gaske sun zo domin nuni akan tabbatar da halascin yin yabo da wake da kida daga Annabi SallallaHu AlaiHi Wasallam matukar ba akan sabon Allah bane, kamar dai yanda yazo cikin hadisin Sayyidah Aisha inda ta ce: (Manzon Allah SallallaHu AlaiHi Wasallam ya shigo wurina a tare da ni akwai wasu kuyangu biyu suna yin kida da wasu korai, sai ya kishingida akan shinfida, sai ya juya fuskansa, sai Abubakar ya shigo, sai ya zungureni ya ce: sarewar shedan a kusa da Annabi SallallaHu AlaiHi Wasallam, sai Manzon Allah SallallaHu AlaiHi Wasallam ya ce masa: “kyale su” a lokacin da hankalinsa ya karkata zuwa wani wurin daban sai na nuna musu ya isa haka sai suka bar wurin, ranar ta kasance ranar sallah ce) [An yi ittifaki akansa].

Annabi SallallaHu AlaiHi Wasallam bai kyamaci kidan da kuyangun biyu suke yi ba, saboda ya tattari kalamai ne na halas, wanda ya kunshi debewa kai kewa a ranar farin ciki, wato ranar sallah, don haka shi kida zance ne, mai kyansa mai kyau ne, mummunansa mummuna ne, ba wani hani a shari’ance na sauraron wake bisa ka’idoji sanannu, kamar dai ya kasance ya wufintu daga mummunan zance da alfasha da motsa sha’awa ko kira zuwa ga hakan, kuma ya zama ba ya kawar da hankali daga gudanar da wajibi kamar lokutan ibada, haka nan wakokin da suke hade da kida, shi kida murya ne mai kyansa mai kyau ne, mummunansa mummuna ne, matukar an kiyaye abubuwan da aka ambata abaya to babu wani hani a shari’ance,  to laifi a saurara.

Share this:

Related Fatwas