Wankar gawa

Egypt's Dar Al-Ifta

Wankar gawa

Tambaya

Mene ne hukuncin zuwan mutumin da ba a bukace shi ba wajen yi wa mamaci wanka?

Amsa

Mustahabi ne halartar wurin yi wa mamaci wanka ya takaita ga mai wanka da wanda zai taimaka masa ne kawai, makruhi ne wanda ba a bukatarsa ya halarci wurin.

 Mustahabi ne mutumin da zai yi wa gawa wanka, da wanda zai taimaka masa su halarci wurin, makruhi ne wanda ba a bukatarsa wajen haka ya halarta, shi dan Adam a asalin dabi’arsa ba ya son kowa ya ga al’aurarsa; a koda yaushe ya kamata a kiyaye masa huruminsa, shin da ransa ne ko bayan ya rasu, lallai shari’ar Musulunci ta yi kira zuwa ga kiyaye alfarmar mamaci, ta kuma kai matuka akan haka, Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Duk wanda ya wanke mamaci, bai yada labarin abin da ya gani a lokacin wankar ba, zai zama ya fita daga zunubansa ya koma kaman ranar da mahaifiyarsa ta haife shi) [Ahmad].

Share this:

Related Fatwas