Wankan gawa

Egypt's Dar Al-Ifta

Wankan gawa

Tambaya

Mene ne hukuncin shari’a wurin halartan wanda ba a bukatarsa a wurin wankan gawa.

Amsa

A kanso takaita yawan wadanda suke yiwa mamaci wanka, hakan ya takaita kawai ga wanda zai taimawaka mai wankan ne, an karhanta halartan wadanda ba a bukatarsu a wurin.

Abin da akafi so shine duk wanda zai halarci wurin wankan gawa ya zama shine zai yi masa wankan, ko wanda zai taimakawa mai yin wankan, don haka aka karhanta halartan duk wanda bai da wani amfana a wurin, domin shi Dan adam a dabi’arsa ba ya son wani ya tsinkayi al’auransa, so da yawa yana son a kiyaye masa al’auransa, shin yana raye ne ko a mace.

Hakika shari’ar Musulunci ta tsayu sosai akan kiyaye harumin mamaci ta tsananta sosai akan haka tare da kwadaitar da hakan, Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Duk wanda yayiwa mamaci wanka, sannan ya kiyaye amanar da ya gani tare da shi, sannan bai tona sirrin da ya gani ba, to zai koma kamar wanda mahaifiyarsa ta haife shi ba tare da zunubi ba) Ahmad.

Share this:

Related Fatwas