Barnatar da ruwa

Egypt's Dar Al-Ifta

Barnatar da ruwa

Tambaya

Mene ne hukuncin wuce gona da iri wurin amfani da ruwa?

Amsa

Allah Maigirma da Daukaka ya yi umurni da kiyaye ruwa da rashin barnatar da ruwan ko amafani da shi ta hanyar da bai kamata ba ko wuce gona da iri ta hanyar amfani da shi ba ta hanyar da ya dace ba, Allah Ta’ala ya ce: (Kada ku yi barna domin Allah baya son masu yin barna)[Al’Araf:31].

Annabi SallallaHu AlaiHi wa’aliHi Wasallam ya ce: (Kuci kusha kuyi sadaka ku sanya tufafin da babu almubazaranci a cikinsa ko jijidakai), Ibn Majah.

Yana daga cikin addu’an Annabi SallallaHu AlaiHi wa’aliHi Wasallam inda yakance: (Rabbi igfir li khadi’ati wa jahli, wa israfi fi amri kullihi.) [An yi ittifaki akansa].

Hakanan hani kan yin barna yazo cikin amfani da ruwa wurin yin tsarki, an ruwaito daga Abdullahi dan Amru dan Aas, Allah ya kara musu yarda, ya ce: Annabi SallallaHu AlaiHi wa’aliHi Wasallam ya ga Sa’ad yana alwala sai ya ce masa: wannan wani irin barna ne? sai Sa’ad ya ce: shin a cikin alwala akwai barna ne? sai Manzon Allah ya ce: (kwarai kuwa akwai, koda kuwa a cikin kogi kake mai gudana) [Ibn Majah].

Hakika jumhor din malamai sun sanya wannan hanin a matakin abun ki, a bisa haka aka karhanta yin barna da ruwa yayin amfani dashi, ya kamata a kan kowani musulmi da ya kiyaye amfani da ruwa ta hanyar da ya dace, tare da nesantar salwantar dashi ta hanyar barna wurin yin tsarki ko wani abu daban.

Share this:

Related Fatwas