Kaffarar rantsuwa

Egypt's Dar Al-Ifta

Kaffarar rantsuwa

Tambaya

Mene ne gwargwadon kaffarar rantsuwa, shin ya halatta a fitar da ita da kima?

Amsa

Ana yin kaffarar rantsuwa ne kawai ga wanda yake rantsuwar gamusi, ana yi wa rantsuwar da mutum ya warware ne kaffara, rantsuwar wasa ba wajibi ne a yi mata kaffara ba.

Kaffarar rantsuwa ita ce: ciyar da muskinai goma, ko yi masu tufafi, wanda kuma bai sami daman yin haka ba, sai ya yi azumin kwanaki uku, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Allah mai girma ba zai yi maku ukuba sakamakon rantsuwar da ba ku kudurce ma’anarta a cikin zukatanku ba, zai yi maku ukuba ne kawai saboda warware rantsuwar da kuka kudurce, kuma aka kulla alkawari da su, idan kun warware ranstuwar da kuka kulla, to dole ne ku aikata abin da zai zamo sanadiyyar yi maku gafara a matsayin kaffara ga rantsuwar, wannan abu kuwa shi ne; ku ciyar da talakawa goma da irin abincin da aka saba da shi, irin wanda kuke ciyar da kawunanku da makusantanku da suke karkashin kulawarku a rana daya, ba tare da barna ko koro ba.. Ko kuma ku tufatar da talakawa goma da irin tufafin da aka saba da shi, ko kuma ku ‘yanta dan Adam daga bauta.. Idan wanda ya yi rantsuwar bai sami daman yin ko daya daga cikin wadannan abubuwa da aka ambata ba, to dole ne ya yi Azumin kwanaki uku. Ana gafarta zunubin rantsuwar da aka warware bayan an yi ta da niyya ne idan aka aikata daya daga cikin wadannan abubuwa, ku kiyaye rantsuwarku kada ku yi rantsuwa a wurin da bai kamata ba, kada kuma ku bar aikata abin da za a gafarta maku idan kun warware ta, lallai da irin wannan bayani ne Allah Madaukakin Sarki yake yi maku sharhi game da hukunce-hukuncensa, domin ku gode akan ni’imoninsa da ya sanar da ku, ku kuma bayar da hakkokinsu kaman yanda suka dace) [al- Ma’ida: 89].

Ana kuma kimanta kaffarar rantsuwa ne da sa’i daya na mafi rinjayen abincin mutanen gari, alal misali kaman: alkama, ko shinkafa, da za a bai wa kowane miskini daya daga cikin miskinai goma, kaman yanda yake a mazhabar Hanafiyya, ana kuma kimanta sa’i ne da kusa kilo (2.5), game da shinkafa ‘yar Misra kuma kimanin kilo (2.75). A mazhabar Shafi’iyya kuma abin da za a fitar shi ne mudu daya na mafi rinjayen abinci mutanen gari, mudu daya yana daidai da rubu’in sa’i ne, ana kuma kimanta shin a giram (510) ga kowane miskini.

Wanda aiki da mazhabar Hanafiyya ya yi masa wahala, babu laifi idan ya yi aiki da mazhabar Shafi’iyya, ya kuma halatta a fitar daga shinkafa ko alkama, kaman yanda ya halatta a fitar da kimar kudinsu duka biyun, watau kimanin abincin da zai ishe miskini mai azumi ya yi buda baki, sai a buga haka sau goma, Allah shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas