Yawan rantsuwa

Egypt's Dar Al-Ifta

Yawan rantsuwa

Tambaya

Mene ne hukuncin yawaita rantsuwa a lokacin saye da sayarwa?

Amsa

Makruhi ne a yawaita rantsuwa a lokacin saye da sayarwa, ganin cewa hakan yana gusar da albarka, yana kuma gusar da ganin girman sunan Allah Madaukakin Sarki daga zukata; lallai Allah mai girma ya bayar da umurnin kiyaye rantsuwa, ya kuma hana yawaita yinta, Allah mai girma da buwaya ya ce: (Ku kiyaye rantsuwarku) [al- Ma’ida: 89], haka ma mai girma da daukaka ya ce: (Kada ku sanya Allah kuna bijiro da shi a cikin rantse- rantesnku) [al- Bakra: 224], akwai Hadisi mai tsarki da ya yi hani akan yawaita yin rantsuwa, musamman a wurin cinikayya, ganin cewa haka yana sance albarka ya kuma dauke ta; Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Rantsuwa tana tafiyar da haja, tana kuma lalata albarka) [al- Bukhari], malaman Fikihu sun bayyana cewa yawaita rantsuwa a lokacin saye da sayarwa makruhi ne; bai kamata mutum ya zama mai yawan rantsuwa ba, sawa’un yana da gaskiya ko ba shi da ita.

Allah Madaukakin Sarki shi ne masani.

 

Share this:

Related Fatwas