Rashin haihuwa
Tambaya
Mene ne hukuncin mata da miji su yi yarjejeniyar cewa ba za su haihu a tsakaninsu ba kwata- kwata?
Amsa
Amsa:
Rashin haihuwa hakki ne na ma’aurata biyu su duka a tare, ya halatta su yi ittifaki akan haka idan har maslahar tasu ce su duka, bai halatta daya ya dauki wannan matakin ba tare da amincewar daya ba; wannan halaccin a matakin daidaiku kenan, saboda dalilai masu zuwa:
Babu wani nassi a cikin Alkur’ani mai girma da ya haramta hana haihuwa, ko takaita shi.
Ittifakin da zai iya zama a wannan yanayi shine kiyasi akan azalo; kuma jamhur din malamai sun hadu akan cewa ya halatta mata da miji su yi azalo idan har su biyun sun amince da haka.
A matakin al’umma kuwa, sam bai halatta a hana haihuwa kwata- kwata ba; domin yin haka zai cutar da daidaiton da Allah ya tsara halittarsa akansa, wannan ya saba da matakan da wasu kasashe suke dauka na kokarin tsarin iyali, saboda dalilai masu zuwa:
Neman kyautata rayuwar al’ummarsu, daidai da nazari da bincike mai zurfi game da karfi da ikon da wadannan kasashe suke da su.
Matakan da shugaba yake dauka suna jujjuyawa ne daidai da maslaha.