Rantsuwa mai halakarwa

Egypt's Dar Al-Ifta

Rantsuwa mai halakarwa

Tambaya

Mene ne hukuncin rantsuwar ganganci?

Amsa

Rantsuwar ganganci da mutum yakan yi da gangan na karya bashi da wani kaffara sai tuba da nadama da istigifari.

Mazhabin mafi rinjayen malamai shi ne babu kaffarar rantsuwar ganganci, wanda mutum kanyi rantsuwa da karya bisa saninsa, sai dai kawai ya tuba yayi nadama sannan yayi istigifari, saboda fadin Ibn Mas’ud Allah ya kara masa yarda, ‘ mun kasance muna ganin samun zunubi akan laifin  da akayi babu kaffara a cikinsa, wato rantsuwar ganganci’ Al’hakeem.

Shafi’iyya sun tafi akan cewa shi rantsuwar ganganci yana wajaba yin kaffara na rantsuwa kamar dai yanda yazo cikin fadin Allah Ta’ala: (Allah baya kamaku da laifin da kukayi na wargi a cikin rantsuwarku sai dai yana kamaku ne da laifin rantsuwar da kukayi nagaske to kaffarar hakan shi ne ciyar da miskinai goma na tsaka-tsakin abin da kuke ciyar da iyalanku ko tufatar da mutane goma ko ‘yanta kuyanga duk wanda bai samu damar yin haka ba to sai yayi azumi na kwanaki uku wannan shi ne kaffaran rantsuwar da kukayi sannan ku kiyaye rantsuwarku haka Allah yake bayyana muku ayoyinsa domin ku kasance masu godiya)[Ma’ida:89]

Bugu da kari akan haka, shi ne mutum ya nuna nadama da tuba na gaskiya ga Allah Ta’ala tare da mayar da hakkokin mutane zuwa garesu a matsayin kaffara.

Share this:

Related Fatwas