wargi ga mai sallah

Egypt's Dar Al-Ifta

wargi ga mai sallah

Tambaya

Mene ne hukuncin wargi ga mai sallah a lokacin da yake yin sallah, kamar dai kyalkyala dariya da makamancin haka?

Amsa

Shi dai yiwa mai sallah wani abu na wargi a lokacin da yake sallah kamar sanya shi dariya ko wani abu da yayi kama da haka haramun ne a shari’ance, kuma duk wanda yake yin haka ya kasance mai laifi.

Ita dai sallah rukuni ce na addini kuma ita ce ginshikin addinin, don haka tana da nata muhimmancin sosai da huruminta, domin ta kasance magana ce da ganawa tsakanin bawa da Ubangijinsa Mai girma da daukaka, don haka babu makawa sai bawa ya nemi hanyar samun tsoron Allah wanda da shi ne wannan ganawar ke daidaita, a wannan maganar da take gudana tsakanin bawa da Ubangijinsa shine ya tabbata a cikin fadin Allah Mai girma: (Hakika muminai sun rabauta wadanda a cikin sallarsu suke nuna jin tsoron Allah) [Mu’uminun:1-2] daga nan ne Musulunci ya hana duk wani abu da zai iya kawo tangarda ga mai sallah wanda hakan zai iya kawo nakasu cikin khushu’in da ake bukatar mai sallah ya zama yana da shi, shin wannan wargin a cikin sallah ne ko a wajenta, bai halasta ga musulmi ya kutsa cikin hurumin sallah  da tsarkin da ke cikinta na sanya mai yinta dariya ba, ko kuma wani abu makamancin hakan, saboda akwai zunubi mai girma a cikin yin haka.

Malaman fikihu ba su rarrabe wargi a cikin sallah da niyyar biyayya ko sabo ba, kawai sun bayar da fatawar hana yin haka ne gaba daya da haramtashi idan ya zama da niyyar gyara ne, don haka sanya mai sallah dariya abun haramtawa ne mai tsanani.

Share this:

Related Fatwas