Barin sallah

Egypt's Dar Al-Ifta

Barin sallah

Tambaya

Mene ne hukuncin mai barin sallah?

Amsa

Sallah ginshikin addini, daya ce daga cikin rukunnan Musulunci, Allah mai girma da buwaya ya bayar da umurni mu tsayar da sallah; Allah mai girma ya ce: (Ku tsayar da sallah, ku bayar da zakka) [al- Baqra: 43], sallah tana da matsayi na musamman a Musulunci, shi ya sanya aka samar mata da rukunnai da lokuta, da farawa da karewa, bai halatta a jinkirta ta ga barin lokacinta ba tare da uzuri na shari’a ba, barin sallah saboda kasala ba ya cikin uzurin shari’a, dole ne a yi duk wanda ba ya yenta da gangan, ko saboda kasala nasiha da kuma kwadaitar da shi akan kiyayeta cikin hikima da wa’azi mai kyau, kaman yanda Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka cikin hikima da wa’azi mai kyau) [an- Nahli: 125], tare kuma da hakuri da juriya akan haka komin tsawon lokaci; kaman yanda Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ka umurci iyalanka da yin sallah, ka kuma yi hakuri da juriyar yin wannan umurnin) [Taha: 132], da kuma yi masa addu’ar shiriya, Allah ya haskaka zuciyarsa da yi masa biyayya; lallai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Lallai addu’ar da mutum yake yi wad an uwansa a boye karbabbiya ce, akwai mala’ika a tsaye a gabansa yana cewa amin a addu’ar da yake yi, a duk sanda ya yi masa addu’ar alhairi, sai ya ce: amin, kai ma kana da kwatankwacinsa), haka ma Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Addu’ar da aka fi saurin amsawa ita ce: addu’ar da mutum yake yi a boye ga wanda baya wurin); lallai yana cikin hali na sabo da yake matukar bukatar wanda zai yi riko da hannunsa a cikin wannan sabon, ba wai yana bukatar wanda zai sanya ya debe kauna ga barin tuba ba, balle ya taimaka masa wajen cigaba da aikatawa kaman shaidan.

Allah shi ne masani.

  

Share this:

Related Fatwas