Lokutan sallah.

Egypt's Dar Al-Ifta

Lokutan sallah.

Tambaya

Mene ne hukuncin bin tsarin jadawalin da hukumar kulawa da sarari ta kasar Masar ta ke fitarwa na lokutan sallah?

Amsa

Ya wajaba abi tsarin da hukumar kulawa da sarari ta kasar Masar ta ke bayyanawa wurin fayyace lokutan sallah, saboda shi tsari ne mai inganci, kuma tabbatacce, kamar dai yanda kwararru suka tabbatar, bai halasta ba, a kowani irin hali, ayi kunnin uwar shegu da irin wannan tsarin da ya fito daga wurin kwararru, saboda wannan aikin yana fayyace lokaci ne na ibada,  don haka ana gina hukuncin Ibada da irin wannan aikin, sannan ya wajaba a nesanci duk wani ra'ayi wanda yake raba kan jama'a, wanda ra'ayin ba ya bisa kan doron ilimi ko asali  ingantacce.

Share this:

Related Fatwas