Boye kayan sayarwa

Egypt's Dar Al-Ifta

Boye kayan sayarwa

Tambaya

Mene ne ukubar boye kayayyakin sayarwa da aka sanyawa tallafi da karkatar da su zuwa kasuwar bayan fage?

Amsa

Samun kayan da aka sanyawa tallafi ba ta hanyar da ta dace ba ko mamaye kayan ta hanyar da ba a halasta ba ko sayar da kayan a kasuwar bayan fage ko boye kayan haramun ne a shari’ance, kuma laifi ne daga cikin manyan laifuka, saboda hakan cutarwa ne da kuma ta’addanci ga wadanda suka cancanci kayan abincin, haka kuma akan dukiyar kowa da kowa, kuma wani salo ne na cin dukiyar mutane da barna, kuma hakan ya sabawa umurnin shugaba wanda Allah Ta’ala ya sanya yi masa biyayya wajibi ne idan ba akan abin da ya shafi sabon Allah ba, wanda hakan ke hade da biyayya ga Allah da Manzonsa Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam), Allah Ta’ala ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi Imani kuyi biyayya ga Allah ku yi biyayya da Manzonsa da kuma shugabanninku) [An-Nisa’i:59]

To fa duk wadanda suke aikata irin wadannan munanan ayyukan na mamaye kayan masarufi da aka sanyawa tallafi tare da sayar da su to shari’a ta yi musu tanajin ukuba har su kasance cikin sanin ciwon kansu daga wannan mugun aikin, an karbo daga Jabeer bin Abdallah – Allah ya yarda da su – sunce  Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce: (Ya kai Ka’abu bin Ujrah, ka sani cewa duk naman da ya ginu da haram ba zai shiga Aljannah ba, wuta ce ta dace da shi, ya kai Ka’abu bin Ujrah, mutane masu komawa ne zuwa ga abu biyu, akwai mai sayen da kansa domin ya ‘yanta, da kuma mai sayar da kansa da kuma halakar da ita) [Imam Ahmad].

Duk mai aikata hakan ya cancanci ukuba na doka da aka tanazar tare da riskan abin da Allah ya yi masa tanaji a lahira.

Share this:

Related Fatwas