Bai wa mayaka mafaka

Egypt's Dar Al-Ifta

Bai wa mayaka mafaka

Tambaya

Mene ne hukuncin bai wa ‘yan ta’adda mafaka da boye su da da’awar cewa ana taimaka masu wajen yin jahadi saboda Allah?

Amsa

Bai wa ‘yan ta’adda mafaka zunubi ne babba, da masu aikata shi suka cancanci la’anta daga Allah Madaukakin Sarki, da’awar cewa yin haka taimako ne akan jihadi, wannan tsagwaron karya ce; lallai abubuwan da wadannan masu laifin suke aikatawa na rusa gidaje da lalata dukiyoyi da kisan rayuka shi ne mafi tsananin zalunci da barna a bayan kasa, wanda shari’a ta zo domin ta hana, ta kuma yaki masu yinsu idan har ba su tuba sun daina cutar da mutane ba, kiran haka da suna jihadi, ba wani abu ba ne banda makirci, saboda su yaudari masu raunin hankali, kuma wajibi ne daukacin al’umma, daidaiku da kungiyoyi da hukumomi dukansu su tsaya su yaki wadannan azzaluman Hawarijawa, sun hana su yin zaluncin da suke yi, kowa ya yi haka daidai da ikonsa da iyawarsa; lallai shari’a ta bai wa mutane umurnin rike hannuwan azzalumi ta yanda ba zai iya yin zalunci da wuce iyaka da yake yi ba, Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi gargadi akan kawar da kai da yi wa azzalumi kowane irin rufi akan zaluncin da yake yi, inda ya sanya yin hakan a matsayin laifin da ya cancanci Allah ya yi hukunci da azaba akansa; domin nuna rashin ko in kula laifi ne da yake bai wa masu aikata laifuffuka daman aikata abin da suka ga dama, yana kuma taimaka masu wajen yada laifin nasu zuwa ko’ina ba tare da shakka ba, Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Lallai idan mutane suka ga azzalumi, ba kuma su rike hannuwansu su hana shi yin zalunci ba, to kuwa nan kusa Allah zai game su da azabarsa) [Ahmad da Abu Dawud, da at- Tirmiziy ya inganta shi, da Ibn Majah, da Ibn Hibban, daga Hadisin Sayyiduna Abubakar al- Siddiq Allah ya kara yarda da shi].

Allah shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas