Kai jana’iza makabarta

Egypt's Dar Al-Ifta

Kai jana’iza makabarta

Tambaya

Mene ne hukuncin raka jana’iza zuwa makabarta, shin hakan yana cikin mustahabai, sannan mene ne ladubban yin haka?

Amsa

Shari’a ta kwadaitar game da raka jana’iza zuwa makabarta, hakan yana cikin mustahabbai a wurin jamhur din malaman fikihu, raka jana’iza yana cikin hakkin Musulmi akan dan uwansa Musulmi, idan za a yi haka ana bukatar al’amurra masu zuwa:

Yi wa mamaci sallah, da daukar gawarsa, da yi mata rakiya har zuwa rufe ta a kabari.

Gaggawar daukar gawa zuwa kabari

Cikakkiyar natsuwa

Rashin ihu da kururuwa

Rashin yi hira akan al’amurran duniya a lokacin raka gawa.

An so a tsaya a gaban kabari a yi Istigfari da addu’ar nema masa rahama da samun tabbacin amsa tambayoyi.

Duk wanda ya cika wadannan zai sami lada mai yawa.

Share this:

Related Fatwas