Bukuwan addini mabambanta

Egypt's Dar Al-Ifta

Bukuwan addini mabambanta

Tambaya

Mene ne hukuncin yin bukukuwan addini mabambanta, kaman bikin tunawa da daren lailatul Qadari, da daren Isra’i da Mi’iraji, da daren Maulidin Annabi mai girma da sauransu?

Amsa

Mene ne hukuncin yin bukukuwan addini mabambanta, kaman bikin tunawa da daren lailatul Qadari, da daren Isra’i da Mi’iraji, da daren Maulidin Annabi mai girma da sauransu?

Amsa:

Bukukuwan addini abu ne da yake mustahabi a cikin shari’ar Musulunci, ba makruhi ba ne, ba kuma bidi’a ba ne, hasali ma hakan yana cikin manyan alamun addinin Allah Madaukakin Sarki: (Duk wanda ya girmama manyan alamomin addinin Allah, to kuwa lallai hakan yana cikin tsoron Allah da take cikin zukata) [al- Hajji: 32], wadannan bukukuwa suna da tasiri a zukata da tarbiyya akan al’umma, abin da yake dawowa da al’umma da amfani na sanin kai da kishin kasa da addini a cikin zukatansu, taruwa saboda wadannan bukukuwa yana haifar da saduwa ta zumunci da biyayya, abin da zai kawar da rashin zumunci da kebancewa ga barin mutane, yana kuma haifar da abubuwa masu amfani da al’umma suke matukar bukatarsu; kuma wannan dam ace na ciyarwa da yada zaman ;afiya da sada zumunci.

Lallai shari’a ta bayar da umurnin tunatar da mutane game da ranakun Allah Madaukakin Sarki a inda mai girma da buwaya yake cewa: (Ku tunatar da su ranakun Allah) [Ibrahim: 5], haka sunna mai daraja ta zo da haka, imam al- Dabaraniy ya ruwaito a cikin littafi “al- Mu’ujamul Ausad” daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Lallai Ubangijinku yana da wasu kyaututtuka a cikin ranakun zamaninku, saboda haka ku bijiro da kawunanku zuwa gare su, duk wanda ya sami wani kasu na wannan kyauta a cikinku ba zai taba tabewa ba har abada).

Game da halaccin maulidin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), saukar masa da wahayi kuwa: An tambayi Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) game da azumin da yake yi ranar litini? Sai ya ce: (Ai a wannan ran ace aka haife ni, a kuma cikinta ne aka aikoni, - ko aka saukar mini da wahayi)..

Share this:

Related Fatwas