Mutuwa a sanadin cutar kansa

Egypt's Dar Al-Ifta

Mutuwa a sanadin cutar kansa

Tambaya

Shin za a iya daukan wanda ya rasu sanadiyyar cutar kansa a matsayin shahidi?

Amsa

Ana fatan samun shahada a lahira ga mutumin da ya rasu sanadiyya cutar kansa; saboda rahamar Allah mai girma da daukaka da zai yi masa, ganin cewa dukan dalili da sanadin samun shahada sun yi tarayya akan radadin da yake samun mutum ya kai shi zuwa ga rasuwa, kuma wadannan dalilan ba a iyakance su, hasali ma suna nuni ne zuwa ga duk wani abu da yake dauke da wannan ma’anar da ka iya auka wa mutane na cututtuka, kuma saboda ganin cewa cutar kansa ta shiga cikin gamammiyar ma’anar harshen a wasu cututtuka, ta kuma yi tarayya da wasu, ta kuma shigar da wasu a cikinta, tare kuma da karin hatsari da tsananin cutarwa, amma fa za a yi wa duk wanda ya rasu saboda kansa duk abubuwan da aka yi wa mamaci na hukunce- hukuncen wanka, likafani, sallah da rufewa a makabarta.

Share this:

Related Fatwas