Kwantar da hankalin mare lafiya.

Egypt's Dar Al-Ifta

Kwantar da hankalin mare lafiya.

Tambaya

Mene ne hukuncin kwantar da hankalin mare lafiya da yi masa addu'a a yayin ziyararsa?

Amsa

An sunnata wa musulmi idan ya shiga wurin mare lafiya domin ya gaishe shi da ya roka masa Allah samun lafiya da kuma abinda zai saukaka masa bakin cikin da yake damunsa, da yaye masa damuwarsa wanda yake da alaka da ciwon da yake damunsa da kuma ajalinsa, kamar yi masa addu'ar tsawon rayuwa, da yayewar  rashin lafiyar da yake damunsa, da makamancin haka, kamar dai yace: "La ba'asa dahurun in sha Allah" ko yace: "Yashfeekallah wa yu'afeeka" ko yace: "Yudawwilul laHu Umraka" da abin da ya yi kama da haka,

Babu shakka lura da halin da mare lafiya yake ciki   tare da rausasa zance da shi tare da cusa masa burin samun dogon rayuwa da samun sauki wani abu ne mai matukar daraja da nuna jin kai da wayewa, domin daga cikin haka akwai shigar da farin ciki da annashuwa a cikin zuciyar mare lafiya, da kuma rausasa zuciyarsa da kwantar da hankalinsa, da karfafa aniyarsa, da sanyawa ransa karsashi wanda hakan ke taimakawa wurin samun sauki daga rashin lafiyarsa.

Share this:

Related Fatwas