Gudanar da ayyuka ba tare da izini ba.
Tambaya
Mene ne hukuncin bude masana’anta ba tare da izinin hukuma ba?
Amsa
Musulunci ya sanya yin aiki da neman halas daga cikin muhimman ayyuka, an karbo daga Al-Mikdad Allah ya kara masa yarda, cewa Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam ya ce: (Wani mutum bai taba cin wani abinci da yake zama mafi alheri gareshi ba kamar yaci abin da hannunsa ya nemo masa, lallai Annabi Dauda: ya kasance yana cin abinci ne ta hanyar abin da hannunsa ya samo masa) Bukhari.
Amma masana’antun da ba ayi musu rijista ba ko kuma wadanda ake kiransu da “tafi da gidanka” wannan ya haramta a shari’ance, saboda cikin haka akwai cutarwa ga makwafta da sabawa doka, haka irin hakan yana nuna yin algus ne na kasuwanci, abin da shari’a ta tabbatar da shi akan haka shi ne haramci, daga Abu Haraira Allah ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam ya ga wani akushi a kasuwa cike da abinci, sai ya shigar da hannunsa a cikin akushin sai yatsun hannunsa suka jike, sai ya ce: (mene ne wannan ya kai mai sayar da abinci?) sai ya ce: ya Manzon Allah, ai ruwan sama ne ya shiga ciki, sai Manzon Allah ya ce: (Inama da ka sanya wanda ya jike a sama domin mutane su gani?!) sai ya ce: (To duk wanda ya ha’incemu to ba ya kan tafarkinmu).