Raya wasu darare da ibada.
Tambaya
Shin ya halasta a raya wasu darare da ibada?
Amsa
Allah ya kebance wasu darare da ranaku da Karin falala da daukaka, domin karfafawa mutane su kara yin da’a, tare da kwadaitar dasu wurin isar da rahama da samun lada zuwa gare su, an so a raya wadannan dararen da ibadu tare da aikata alheri, daga cikin irin wadannan ranakun akwai: Daren lailatul kadr, da daren karamar sallah, da daren babbar sallah, da daren goma da watan Zul Hijjah, da dararen goman karshe na watan Ramadan, da kuma daren 15 ga watan Sha’aban, da daren ranar Arafat, da kuma daren ranar Jumu’a, da daren farkon watan rajab.