Tsayuwar mamu tare da liman

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsayuwar mamu tare da liman

Tambaya

Yaya mamu zai tsaya tare da liman idan mamu din mutum daya?

Amsa

Sunna ita ce mamu guda daya ya tsaya a daman liman, mustahabi ne ya dan yi baya kadan ta yanda za a iya bambance tsakanin mamu da liman, an ruwaito Hadisi daga Ibn Abbas (Allah ya kara yarda da su) ya ce: (Na kwana a gidan innata Maimuna, sai Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi sallar Issha’i, sannan ya zo ya yi sallah raka’a hudu, sannan ya yi barci, sannan ya tashi, sai na tashi tare da shin a tsaya a hagunsa, sai ya sanya ni a damansa) [al- Bukhari da Muslim].

Saboda haka idan ya tsaya a hugunsa, ko a bayansa ana son a gyara masa, shin liman ne zai yi gyarar ko wanin liman din, idan aka gabatar da sallah a haka kuma sallar ta yi, ba za ta baci ba, sai dai bah aka aka so ba.

Share this:

Related Fatwas