Sauya abu mare kyau

Egypt's Dar Al-Ifta

Sauya abu mare kyau

Tambaya

Shin da gaske abubuwan da kungiyoyin ‘yan ta’adda suke yi shi ne “bayar da umurni da aiki mai kyau da hana mummunan aiki?

Amsa

Canja abu mara kyau abu ne da shari’a ta nemi a yi, amma fa wadanda za su yi haka su ne wadanda suka cancanta da kuma wasu sanannun sharudda, kuma idan har aka aiwatar da wannan sauyi akwai abubuwa masu kyau da suke faruwa sakamakon kawar da munkari, ta kuma yiwu a sami cutarwa sakamakon wannan sauyi, Kaman daukan makami da sauransu, saboda haka ne shari’a ta sanya matakan wannan sauyin, malamai sun yi maganganu dalla- dalla akan abubuwan da nassoshi suka zo da su a dunkule.

Idan har akwai yiwuwar a dauki makami, to irin wannan sauyin an mika shi ne a hannun shugaba, gudun kada kawar da wannan munkarin ya kai zuwa ga aukuwar wani abu da muninsa ya fi na munkarin da ake son a kawar, a cikin hujjojin da suke tabbatar da haka akwai fadakarwar da Allah Madaukakin Sarki ya yi a inda yake cewa: (Kada ku zagi abubuwan da ake bauta wa wadanda ba Allah, gudun kada hakan ya kai wuwa ga zagin Allah saboda mayar da martini ba tare da sani ba) [al- An’ami: 108], a nan an gabatar da tunkude barna akan jawo maslaha.

Haka ma inkarin munkari da hannu abu ne da ya kebanci shugaba majibincin al’amari, zai kuma zama da harshe ne ga dukan mutane, saboda haka dole ne Musulmi ya sauya shi ta dukan fuskokin da zai iya; ya kuma zama mai rausasawa wajen wannan sauyi, domin hakan ne zai fi sanya a karbi sauyi, a kuma kawar da munkarin, zai iya neman taimako da wata hanyar idan babu tsoron aukuwar wata fitina ta daukan makami da yaki, idan har ya gaza wajen kawo sauyi, to sai ya sanar da shugabanni, ko hukumomin da abin ya shafa, idan kuma duka haka ba su samu ba sai ya ki abin a zuciyarsa.

Share this:

Related Fatwas