Yin kyara ga mare lafiya.
Tambaya
Mene ne hukuncin wanda yake yiwa waninsa tsiyan ciwo”kyara”
Amsa
Yin zagi ko tsiya ko kyara sakamakon afkuwan masifa da jarabta da yake fadawa mutane daga ciki akwai mutuwa ba ya cikin kyawawan dabi’u, duk wanda ya yiwa waninsa kyara saboda mutuwa hakan baya cikin kyawawan dabi’u, shi kansa mai yin kyaran mutuwar wani zai mutu, kamar dai yanda waninsa shima ya mutu, shin mutum zaiyi farin ciki idan akace masa: Lallai wane zaiyi farin ciki idan ka mutu?! Hakika Annabi SallallaHu AlaiHi Wasallam ya ce: (Kada ka bayyana kyara “zagi” ga dan’uwanka, sai Allah ya bashi lafiya kai kuma ya jarabceka dashi) Tirmizi.
Shidai zagi da nuna jin dadi bisa masifun da suka samu mutane – ko ta yaya ne - ya sabawa dabi’un Annabta mai girma, da kuma dabi’ar mutumtaka na zahiri, a lokacin samuwar masifu ya wajaba a wa’azantu da shi ne ba farin ciki ba.