Bayar da zakka ga mara lafiya.

Egypt's Dar Al-Ifta

Bayar da zakka ga mara lafiya.

Tambaya

Shin ya halatta a dibi kudaden zakka a bai wa masu fama da ciwon koda, ko masu fama da cutar karanci ko gurbacewar jini, wadanda suke bukatar a sanya masu ledojin jini a koda yaushe kuma ba su da halin saye?

Amsa

Shari’ar Musulunci ta halatta a dibi kudaden zakka a bai wa masu fama da ciwon koda, ko masu fama da cutar karanci ko gurbacewar jini, wadanda suke bukatar a sanya masu ledojin jini a koda yaushe kuma ba su da halin saye; domin Allah mai girma da buwaya ya sanya talakawa da miskinai a sahun- gaba na mutane takwas da za a ba su zakka; Allah mai girma ya ce: (Ai ita zakka da ma ana bayar da ita ne kawai ga talakawa, da miskinai, da masu aikin tattarata da rarrabata, da wadanda ake tarerayar zukatansu, da wajen ‘yanta bayi, da wadanda ake binsu bashi, da kuma wajen daukaka kalmar Allah, da matafiyi, wannan farali ne daga Allah, lallai Allah yana da cikakkiyar masaniya akan komai, shi ne kuma mai cikakkiyar hikima) [at- Tauba: 60]; wannan ya zo ne saboda ya kara bayyana cewa su ne a sahun gaba cikin wadanda suka cancanta a ba su, kuma asali dole ne a samar masu da abubuwan da suke bukata wadanda rayuwa ba za ta yiwu ba sai da su, irinsu wurin zama, da abinci da karatun ‘ya’yansu da magani, musamman idan suna cikin halin rashin lafiya mai tsananin da magungunansu yake da matukar tsada, kaman masu fama da cutar koda, samar masu abubuwan da dole sai da su ne rayuwa za ta yiwu ya hada samar masu da ruwa, da kudaden magani, saboda su ma su ji dadin rayuwa kaman yanda masu lafiya suke ji, saboda haka bukatunsu sun shiga cikin zakkar da mawadata suke fitarwa, tare da la’akari da tsare- tsare da dokokin da aka tabbatar a ire- iren wannan al’amari.

 

Share this:

Related Fatwas