Bayar da zakka domin sayen magungun...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bayar da zakka domin sayen magunguna

Tambaya

Mene ne hukuncin bayar da zakka domin saya wa talakawa marasa lafiya magunguna?

Amsa

Ya halatta a bayar da kudin zakka a sayi magunguna ga talakawa marasa lafiya, bai wa talakawa da mabukata abubuwan da suke matukar bukata na tufafi da abinci da wajen zama, da abubuwan rayuwa da karatu da lafiya da sauran al’amurran rayuwa, su ne abubuwan da wajibi ne a muhimmanta su a fara gabatar da su akan komai, domin zartar da babbar manufar shar’anta zakka da hikimarta, wadda Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi nuni zuwa gare ta a inda yake cewa: (Za a karba daga hannun mawadatan cikinsu, a rarraba wa matalautan cikinsu) [al- Bukhari da Muslim]; a nan samar da magunguna ga talakawa marasa lafiya ya shiga ciki.

Share this:

Related Fatwas