Bayar da zakka ga hukumomin da suke...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bayar da zakka ga hukumomin da suke rarraba abinci da magunguna

Tambaya

Mene ne hukuncin sayen kayan abinci da magunguna da kudin zakka domin bayarwa ga mutanen da suke bukatar abinci da magunguna?

Amsa

Ya halatta a bayar da zakkar kudi domin biyan bukatun talakawa da miskinai, ta hanyar samar masu da abin da suke bukata na kayayyakin abinci ko magunguna; duk da cewa ita zakka a asali tana kasancewa ne da nau’in dukiyar da zakkar ta wajaba, sai babban manufarta it ace biyan bukatun talakawa da mabukata, kuma a duk sanda jinsin da aka fitar wa da zakka ya zama shi ne ya fi dacewa da bukatunsu, ya kuma fi amfanarsa, to wannan ya fi kusa da cimma manufar yin zakka.

 

Share this:

Related Fatwas