Sallar Asubahi ga mutumin da zai yi tafiya kafin lokacinta
Tambaya
Yaya mai tafiya kafin sallar Asubahi zai gabatar da sallar Asubahi?
Amsa
Idan Musulmi ya kama hanyar yin tafiya zuwa wurin aikinsa kafin kiran sallar Asubahi, sannan lokacin sallar ya shiga: idan ya san cewa zai iya kai wa wurin da zai iya gabatar da sallah da cikakkun sharudda da rukunnanta kafin rana ta fito; to ya jinkirta har sai ya isa. Amma idan ya san cewa ba zai kai ba sai bayan fitowar rana, kuma zai yi wahala ya iya gabatar da sallar cikin cikakkun sharudda da rukunnanta a lokacin da yake cikin abin hawa; to ya yi sallar gwargwadon abin da zai iya cikin sharudda da rukunnai, an so ya sake maimaita sallah idan lokacin bai fit aba, ko ya rama idan lokaci ya fita.