Camfi a wasu ranaku da lambobi

Egypt's Dar Al-Ifta

Camfi a wasu ranaku da lambobi

Tambaya

Mene ne hukuncin bakacen sharri a lokacin ganin wani lamba na musamman ko zuwan wata rana ko wani dangantaka kayyadajjiya, kamar dai wanda ake yin camfi a cikinsu?

Amsa

Shi dai camfi na wasu lambobi da na wasu ranaku ko wasun haka ababen hani ne a shari’ance, saboda al’amura suna gudana ne bisa umurnin Allah Mai girma, kuma babu wata alaka tsakanin wadannan al’amura da wani alheri da zai samu mutum ko wani sharri da zai same shi, daga cikin abin da aka sani a shari’ance shine hani akan yin camfi da tsammanin sharri gaba daya, kasancewar hakan ayyukan jahiliyya ne, kamar dai yanda hanin hakan yazo a wasu lokuta da watanni kebantattu, daga cikin hakan akwai wanda yazo a “sahihaini” daga Abu Huraira, (Allah ya kara masa yarda), daga Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Babu wata annoba babu wani canfi ga watan safar babu wata mujiya da ke cutarwa), hikimar da yake cikin wannan hanin shine hana abin da camfi ya kunsa da tsammanin sharri yana daga cikin munanawa Allah Madaukakin Sarki zato, tare da haifar da jinkirta himma a cikin aiki, hakanan hakan yana daidaita tunanin zuciya da haifar da bacin rai da dimuwa.

Allah Madaukakin Sarki ne mafi sani.

Share this:

Related Fatwas