Canfin kwanaki da alkalumma

Egypt's Dar Al-Ifta

Canfin kwanaki da alkalumma

Tambaya

Mene ne hukuncin mutumin da ya zaci faruwar sharri kawai saboda ya ga wata lamba, ko fuskantowar wata rana, ko nunasabar wani abu, abin da ake kira da “canfi”?

Amsa

Amsa:

Shari’ar Musulunci ta hana yin canfi da alkalumma da kwanaki da wasunsu; saboda dukan al’amurra suna gudana ne da irin yadda Allah Madaukakin Sarki ya kaddara, wadannan abubuwa ba su da jibi da wani alhairi ko sharri da zai sami dan Adam, abin da kowa sani ne cewa shari’a ta haramta canfi, ta kuma dauke shi a matsayin wata tada ta zamanin jahiliyya; haka ma an ruwaito Hadisai daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da suke hana yin canfi a wasu kebantattun lokuta da watanni; Hadisi ya zo a cikin sahihul Bukhari da Sahihu Muslim daga sayyiduna Abuhuraira (Allah ya kara yarda da shi), daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Babu wata cutar da take zarcewa daga jikin wanda yake dauke da ita zuwa waninsa akan karan –kanta,  babu kuma wata macijiya a ciki da take sarar dabbobi da mutane da ake canfi da ita, babu kuma wani tasiri da mujiya yake yi a karan kanta), hikimar da take tattare da wannan hanin shi ne hana abin da yake tattare da canfi na munana wa Allah Madaukakin Sarki zato, da lalata himmar gabatar da aiki, haka ma da irin yanda hakan yake ruda zuciya ya sanya ta cikin damuwa da rudu.

Allah Madaukakin Sarki shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas