Rashin kula da aiki

Egypt's Dar Al-Ifta

Rashin kula da aiki

Tambaya

Mene ne hukuncin mutumin da ba ya kulawa da aikinsa, ko alhakin da ya rataya akansa?

Amsa

Ma’aikaci mutum ne da aka amince masa akan aikin da aka daura masa, rashin gabatar da wannan aiki Kaman yanda aka bukata, bayan kuma ya amshi albashi akan haka haramun ne a shari’ar Musulunci; nuna halin ko’in- kula a aiki, da rashin yinsa kaman yanda ya kamata cin amanar al’umma ne, yana kuma cikin algushi da makirci da yaudara, kuma hakan saba wa doka ne da hukuncinsa yake hannun shugabannin gudanarwa, domin dokokin sun tsananta hukunci akan wanda ya nuna rashin kulawa da aikinsa, a gefe daya kuma ma’aikaci zai sami lada idan ya kyautata aikinsa ya yi saboda Allah.

Share this:

Related Fatwas