Hasashen kirkiran addini

Egypt's Dar Al-Ifta

Hasashen kirkiran addini

Tambaya

Mene ne alamun da suke nuna cewa kungiyoyin da suke kafirta Musulmai suna bin wasu karantarwa da suka saba da karantarwar addinin Musulunci mai daraja?

Amsa

Addinin Musulunci wata dangantaka ce mai daraja tsakani bawa da Ubangijnsa, ilimi da yake da asali, da kuma manazartansa, ana daukansa ne akan tsari da asalinsa da a kuma gaban malamai masana; babban sifarsa ita ce shi karbabbe ne mai nagarta a wurin masu shi.

Ta yiwu mutum ya gaza wajen koyon addini karkashin wadannan ka’idojin, hakan ya kais hi ga gujewa zuwa ga wasu ‘yan dubarbaru da zai fage da su wajen mas’alar neman ilimi, kuma wannan ne abin da masu tsattsauran ra’ayi suke yi; inda kungiyoyin ‘yan ta’adda suke yunkurin samar da makwafin da zai kwafe matsayin wasadiyyar addini, da abubuwan da al’umma suka dogara da su a tsawon karnoni masu yawa wajen kafa hujjoji, da hanyoyin fahimtarsu, da kuma salon aiki da su, da malamansu da kuma hanyar da ake bi a samar da su, hasali ma sun sauya abubuwa na shugabannin malamai masu daraja da tsarki, da wasu abubuwan na karya, wannan din wani nau’i ne da ake kira yaudarar addini, ko addinin rudu; shi ne kuma abin da muke nufi da kirkiran addini, inda mutum ko jama’a za su samar wa kansu da madogara da suke kishiya ga madogarar addini, da manazarta da suke sabanin manazartan addini, da ma asali da ya saba da asalin ingantaccen asalin addini, inda za su cigaba da habaka su a cikin al’umma masu tasowa, inda za su sami rarrabuwar kawuna mai tsanani, kai da bata mai nisa, misalign haka shi ne mutum ya tsaya a gaban madubi, hotonsa ya bayyana a ciki, ya kuma zaci cewa hoton shi ne asali, wannan shi ne ake kira da makuwa, zai iya zama shi mutumin iya gaskiyarsa kenan a zatonsa, sa’ilin da abin da yake a fili shi ne sabanin abin da yake zato, wato shi ne asalin, na cikin madubin hotonsa ne kawai.

Addinin kirkira shi ne mayar da addini zuwa ga wasu surori na zahiri a mafi yawan lokuta, wanda da zaran an gansu to mai su shi ne mai addini, shi ne yake akan gaskiya da daidai, duk wanda ya saba masa kuma yana kan bata, a kuma jefe shi da bidi’a, kai ka ce gaba dayan mutane (Musulmai) suna gefe, wasu kuma suna wani gefe, koda kuwa suna riko da wasu alamomin addini da wasunsu suke hukunci da Musulunci akan wadanda suke da su.

Share this:

Related Fatwas