Musulunci da sauran addinai
Tambaya
Shin akwai wani gaba ne kwantacciya tsakanin Musulunci da sauran addinai..?
Amsa
Babu wani gaba tsakanin Addinin Musulunci da sauran addinai daban - daban, ai lamarin ma akasin yanda ake zato ne, saboda shi Musulunci addini ne na zaman lafiya, sannan Annabin Musulunci Annabin rahama ne (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam); domin Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Ba mu aiko ka ba face ka zamto rahama ga dukkan talikai) [Al-anbiya: 107], haka nan Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Cikakken Musulmi shi ne wanda mutane suka kubuta daga harshensa da hannunsa, shi kuma mumini shi ne wanda mutane suka aminta da shi a jinane da dukiyoyinsu) [an-Nasa’i], akwai girmamawa sosai da yin tarayya da taimakekeniya da Musulmi sukan yi da waninsa daga cikin mabiya wasu addinai daban, wato dai kamar raya kasa, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Shi ne wanda ya samar da ku daga kasa ya kuma sanya ku masu rayata da zama cikinta) [Hud: 61], abin nufi da raya kasa anan shi ne mayar da hankali da yin aiki wurin tabbatar da kyawawan dabi’u madaukaka da aka tsayu a kansu, kamar a ce kiyaye mutum da hidimta masa, misali ta bangaren kula da kiwon lafiyarsa na jikinsa da kwakwalwarsa, haka nan ta bangaren tattalin arziki, zamantakewa, da kyawawan dabi’u, haka nan kamar kiyaye mahalli da dangoginsa da raya mahallin, bisa haka ne muke lura da kiyaye dabbobi da tsirrai da sauran sandararrun abubuwa, haka nan kamar kin yin barna a doron kasa ta kowace irin fuska, haka nan kin yin zalunci, tare da kokarin tsayar da adalci, tare da mayar da hankali wurin taimakawa mai rauni, haka nan kamar daukan nauyin masu karamin karfi da taimakekeniya da juna musamman lokacin samuwar ibtila’i da sauran abubuwa masu kama da haka daga cikin manyan dabi’u da duk mai hankali ya san da su.