Musulunci bai yadu da kaifin takobi...

Egypt's Dar Al-Ifta

Musulunci bai yadu da kaifin takobi ba.

Tambaya

Shin gaskiya ne cewa Musulunci ya yadu da kaifin takobi ?

Amsa

Musulunci bai yadu a tsakanin mabiyansa da kaifin takobi ba ko kadan, sai dai ya yadu ne ta hanyar kira zuwa ga Allah cikin hikima da kyakkyawan wa’azi da kyawawan dabi’u na Musulmai tare da iya mu’amalarsu da sauran halittu, sannan da kyakkyawan imamninsu da Ubangijin talikai, daga cikin dalilai bayyanannu akan haka akwai: da yawan malamai da shugabannin Musulmai ba su kasance daga yankin tsibirin Larabawa ba, kuma ba su kasance daga cikin ‘ya’yan Larabawa ba tun asali, da a ce an cusa Musulunci da karfin- tuwo ne, to da ba su yi fice sun bayyana a fagagen ilimi da fannoni daban daban ba har suka kai kololuwar sani da kwarewa, daga cikin mafi shaharar wadannan shugabannin Imamul A’azam Abu Hanifa Al-nu’man, ma’abocin mazhabar Hanifiyya, da Imamu Bukhari, mai littafin Sahihul Bukhari, haka nan Babban masanin harshen Larabci nan wato Amru bin Usman, wanda aka fi sani da Sibawaihi, mai babban littafin mai suna “Al-kitab” haka nan dalibinsa Al-imam Abul Hasan Al-akhfash, tare da Hujjatul Islam Abu Hameed Al-Gazali, haka nan As-sheikh shugaba masanin falsafa kuma likita Ibn Sina’a, sannan kuma akwai Al-farabi babban masanin falsafa, akwai Al-khawarizmi masanin ilimin falaki da lissafi da taswirar kasa da sauransu. To da a ce kakannin wadannan malaman sun shiga Musulunci da tilasci bisa kaifin takobi, to ai da ‘ya’yansu da jikokinsu ba su yi sha’awar Musulunci ba, kuma da ba su koye shi ba har su rinka ba shi kariya suna yada shi a dukan sasanni.

Share this:

Related Fatwas