Musulmi mai wuyar sha’ani

Egypt's Dar Al-Ifta

Musulmi mai wuyar sha’ani

Tambaya

Mene ne ya sanya malamai suke cewa: Musulmi mutum ne mai wuyar sha’ani?

Amsa

Wannan kalmar ta zo domin ta bayyana wahalar da yake cikin fitar da Musulmi daga da’irar Musulunci, sai idan sharudda uku masu wahalar tabbatuwa sun faru, babu yanda za a yi a sifanta Musulmi da kafirci sai sun tabbata, tabbata kuma na hakika ba na tunani, ko fahimtar wasu ba, wadannan sharudda sun hada da: ya zama da kansa yana nufin yin kafircin, yana kuma sane da haka, kan cewa wannan aiki nasa, ko maganarsa kafirce wa Allah ne, ya kuma zama ya yi hakan ne da zabinsa, ba tilasta masa aka yi ba, idan aka rasa sharadi daya cikin wadannan sharudda, to abu ne mai matukar wuya a iya fitar da shi daga addini, a sifanta shi da kafirci, ta nan ne malamai suka yi amfani da wannan kalma ta “Musulmi mutum ne mai wuyar sha’ani”, saboda wahalar tabbatuwar wadannan sharudda, malamai sun yi bayanai masu fadi akan wadannan sharudda a cikin litattafan fikihu da sauransu. Kai koda ma wadannan sharudda sun samu, to zartar da wannan hukunci aiki ne na sashen shari’a, babu wani mutum da ya halatta masa ya yi hukunci da kafircin wani sai alkalin da hukuma ta amince da shi; ganin cewa irin wannan hukunci yana haifar da wasu hukunce- hukuncen a duniya masu matukar muhimmanci, a cikinsu akwai wadanda suke da jibi da dukiyoyi da gado, kafiri ba ya gadon mumini, haka ma mumini ba ya gadon kafiri, da kuma raba tsakanin mutum da matarsa, da sauran hukunce- hukunce, saboda haka, auka wa wannan fage abu ne mai matukar wahala, kuma fitina ce babba.

Share this:

Related Fatwas