Tsanantawa a cikin lamuran addini.

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsanantawa a cikin lamuran addini.

Tambaya

Mene ne hukuncin tsanantawa a cikin lamuran addini? Shin akwai misali akan haka?

Amsa

Lallai shi tsanantawa a cikin addini abu ne na zargi, hakika ma’anarsa ya bayyana ne a wurin masana a tuntuni, hakika Al’kur’ani ya yi nuni akan haka cewa tsanantawa wani abu ne da ya yadu a cikin al’ummun da suka gabata, domin irin hakan ne ma ya jawo ko ya zama sanadin jawo tsauri ko kyekyashewar zuciya da tsanantawa ga su wadannan al’ummun, Allah Ta’ala ya ce: (Kace musu ya ku Ahalul Kitabi kada kuyi shisshigi a cikin addininku idan ba akan gaskiya ba) [Ma’adah:77].

Sannan Annabi SallallaHu AlaihI wasallam ya yi nuni zuwa ga hakan a gargadin da ya yiwa wannan al’umma kan tsanantawa, da nesantar abin da zai kai ga fadawa cikin kuskure irin wanda al’ummun baya suka fada na shisshigi da kutsawa cikin lamuran zafafawa da tsanantawa ko wuce gona da iri, sai ya ce: “ Kar ku tsanantawa kawunanku domin za a tsananta muku, saboda wasu mutane sun tsanantawa kawunansu sai shi ma Allah ya tsananta musu, wadancan gurabunsu ne da suka wanzu a wuraren bauta da gidajensu”.

-Daga cikin misalan hakan na baya shi ne kissar ma’abota Saniya, kissar da Al’kur’ani Maigirma ya ambata, wanda hakan yana nuni ne akan tsanantawa da yin dagawa irin na bani Isra’ila, a lokacin da Allah ya umurce su da su yanka Saniya, abin da ya kamace su da suyi shi ne su bi umurnin da aka basu, sai dai sunki yin hakan, sai suka fifita jiji da kai da tsanantawa wurin neman irin saniyar da za su yansa da kamanninta, a duk sanda suka zafafa wurin tambayar kamannin saniyar sai su kara tsanantawa kawunansu, wurin neman Karin kamanni, a karshen ayoyin sai suka ce: (To a yanzu ne kazo da gaskiya sai suka yanka saniyar ai da kamar ba za su aikata abin da aka umurce su da shi ba)[Albakara:71]

 Duk fa da cewa zancensu na: “Yanzu” ya bayyana mana gaskiyar zancen yanda su bani Isra’aila suke tsaurara zancensu ga Annabi Musa kenan, saboda ya bayyana musu gaskiya akan duk abin da suka bukata a aikace.

Share this:

Related Fatwas