Shisshigi a cikin lamuran mutane

Egypt's Dar Al-Ifta

Shisshigi a cikin lamuran mutane

Tambaya

Mene ne hukuncin yin shisshigi a cikin lamuran mutane?

Amsa

Girmama sirrikan mutane wajibi ne na shari’a da mutumtaka, don haka ne ma musulunci ya haramta tozarci da yiwa mutane yafice, Allah Ta’ala ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi Imani kada wani sashenku su tozarta wani sashe watakila su kasance sun fisu alheri hakanan kar wani sashe na mata su tozarta wani sashe na mata watakila su kasance sun fisu alheri, kada ku yi wa kawukansu yafice kada ku yi wa juna lakabi mare kyau kaicon suna na fasikanci bayan yin Imani duk wadanda ba su tuba daga irin haka ba to ire- irensu su ne azzalumai)  [Hujurat:11]

Allah Mai girma da Buwaya ya ce: (Kada ku yi ta’addanci lallai Allah ba ya son masu yin ta’addanci) [Albakrah: 190].

Annabi sallalaHu AlaiHi Wasallam ya ce:  “Abu mafi nauyi a ma’aunin mumini ranar alkiyama shi ne kyakkyawan dabi’u, Allah ba ya son mai mummunan dabi’a da bayyana mummunan zance” Bukhari.

  Annabi sallallaHu AlaiHi Wasallam ya ce: “Yana daga cikin kyawun Musuluncin mutum ya bar abin da babu ruwansa” Tirmizi, yin ta’addanci da cutarwa ga wani – koda kuwa da kalma ce- to abun ki ne a shari’ance.

Share this:

Related Fatwas