shiga cikin gasa

Egypt's Dar Al-Ifta

shiga cikin gasa

Tambaya

Mene ne hukuncin shiga cikin gasan jiran tsammani

Amsa

Daga cikin abin da aka tsara a shari’ance shi ne haramcin lido da caca da kuma rehu, Allah Ta’ala ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi Imani da Allah ku sani cewa ita giya da caca da gumaka da kibau na camfi kazanta ne daga cikin ayyukan shedan don haka ku nesancesu don kwa rabauta) [Ma’idah: 90] Allah Subhanahu wa Ta’ala yana cewa: (Kada kuci dukiyoyinku a tsakaninku da barna ku sanya dukiyar a hanyar masu hukunci domin kuci wani yanki na dukiyar mutane da zunubi alhali kuna masu sanin haka) [An-nisa’a: 188], Allah Ta’ala ya ce: (Ya ku wadanda kukayi imani kada kuci dukiyoyinku a tsakaninku da barna sai dai fa idan ta hanyar kasuwanci ne a bisa amincewa a tsakaninku) [An- Nisa’i: 29]

Irin wannan gasar idan har ta zama akwai sanya kudi a ciki to ta zama caca da rehu irin wanda aka hana, saboda duk wadanda suka shiga cikin gasar sun sanya kudi, sannan wanda yaci cacar shi zai kwashe kudin da aka sanya gaba daya.

Amma idan ya zama shiga cikin gasar ba da kudi ba ne, to hukuncin shari’a akansa shi ne halasci.

A bisa haka, shiga cikin gasa na rehu kamar na wasanni da babu bukatar sanya kudi a ciki ya halasta, matukar wanda ya shiga cikin gasar ya shiga ne bisa masaniya da kuma nazari akan yanda ya kamata lamura su kasance.

Share this:

Related Fatwas