Sharudan yin aikin da’awa

Egypt's Dar Al-Ifta

Sharudan yin aikin da’awa

Tambaya

Mene ne sharudan yin aikin da’awa a Addinin Musulunci?

Amsa

Ya wajaba ga mai kira zuwa ga Allah ya zama mai basira, Allah Ta’ala yana fadi a cikin hakkin Annabi SallaHu AlaiHi wa sallam da kiransa : (Ka gaya musu wannan ita ce tafarkina da nake kira zuwa ga Allah da ita a cikin basira ni da wanda ya bi tafarkina) {Yusuf 108} Don haka ya wajaba mai da’awa ya kasance mai kulawa da lamura sosai kuma mai la’akari da manufofin shari’a, kuma ya kasance masani akan matsalolin al’ummarsa, hakanan ya kasance mai yawan bincike akan ilimomin shari’a da na harshen Larabci, tare da kasancewa kwararre a wani fannin na ilimi don ya kasance akan ilimi bisa ayyukan da yake gabatarwa, sannan ya kasance mai tsarkake niyyarsa a wurin kiransa zuwa ga Allah, ba domin abun duniya ba ko kuma wata bukata ta kashin kai. Allah Ta’ala yana cewa : (Ba a umurcesu ba sai dai don su bautawa Allah suna ma su tsarkake niyyansu wurin bauta mishi cikin addinin) {Albayyina 5}, an karbo daga Annabi SallaHu AlaiHi wa sallam yana cewa : (Lallai Allah ba ya karban wani aiki sai dai fa wanda  ya tsarekake niyya a ciki domin Allah, kuma aka nemi yardansa a cikin aikin) [An’nasa’i]

Hakika wannan yana daga cikin muhimman sharudan da suka rataya ga mai da’awa ya kasance abin koyi bisa ga abin da yake kira zuwa gare shi, kamar ayyukansa da zantuttukansa da dabi’unsa da mu’amalarsa, sannan ya kasance masani ne kan yanayin rayuwar da ake ciki, tare da sanin al’adun mutane da halayyar mutane, don kar ya fuskanci mutane da maganar da za ta kai ga karyata Allah da Manzonsa SallaHu AlaiHi wa sallam, domin Annabi SallaHu AlaiHi wasallam shi ne abin koyi ga kowa wurin da’awa, Allah Ta’ala yana cewa : (Hakika kuna da abin koyi mai kyau a wurin Manzon Allah) [Al-ahazab: 21], Dabi’un Manzon Allah sallaHu AlaiHi wasallam sune Alkur’ani, don haka ya kasance jagoran ma su kira zuwa ga Allah Subhanahu.

Share this:

Related Fatwas